الأحد، 27 يوليو 2008

RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI #2


RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI #2.

Gabatarwa:
Bayanda a kasidar data gabata mukai takaitaccan bayani kan yadda musulunci ya tsara yadda ya kamata rabuwar aure ta kasance, da kuma yadda ya baiwa ko wanne bangare na ma'aurata 'yancinshi, da kuma yadda bayanai suka gabanata na cewa babu wani tsari da yayiwa mabiyanshi irin wannan tsarin inba musulunci ba. to ayau za muyi bayani abinda Allah Maigirma da daukaka ya sawwake mana na yadda Idda kuma zata kasance bayan anyi saki ko anrasu Allah yai mana jagora amin, asha karatu lafiya.

Kadan daga Hikimomin Idda.

Yana daga cikin hikimomin da Allah ya sanya cikin Idda kada adauki dan-wani gida akai wani gidan, domin idan mutun ya rabu da maidakinshi takan yiwu a wannan makon ansami juna-biyu, idan tai aure batare da yin iddaba bayan kwana biyu ko uku ko makamantansu da sakinta shikenan ta tauki dan-mijinta na farko ta kai gidan mijinta na biyu wanda yake wannan bakaramin zunubi bane da barna a harkokin zamantakewarmu, saboda haka musulunci ya tabbatar da cewa ba zatai aure na biyuba sai antabbatar da bata da juna biyu saboda haka aka shar'anta takaba, saidai kawai idan aka saketa kafin asadu to awannan lokacin babu wata Idda da zatayi, kamar yadda bayanai zasu zo nan gaba kadan idan Allah ya yarda. Haka kuma yana daga cikin Shar'anata Idda fatan bijin ya maida ita matar ta shi kafin ta kammala iddar idan sakin baikai ukuba, kamar yadda bayani ya gabata a makalar farko inda muka kawo fadin Allah Maigirma da daukaka " Baka saniba ana fatan Allah ya aiwatar da wani al'amari" Suratut-Talaq, aya ta 1, domin ba din da iddarba da shikenan kana sakinta yau gobe sai wani ya aura taimaka Fintinkau. Kazalika yana daga cikin manufofin yin Idda juyayin megidanta daya rasu ko dako basu taba saduwaba, kamar yadda bayani ya gabata arubummu metaken "Takaba a Musulunci". Saboda haka ko iyanan muka dakata kasan Allah Maigirma da taukaka ya sanya hikimomi masu tarin yawa cikin Idda, munsan su duka ko bamu sansu ba. Allah mungode maka.
Karkasuwar Idda a musulunci
.

Idda ta kasu kashi biyu a musulunci, wato Iddar mamaci wacce muke ce mata takaba, da kuma Iddar Saki. Itadai iddar mamaci\Takaba mungudanar da bayanai akanta, saboda haka awannan karon bayanai zasu kasance ne kan "Iddar Saki"! Allah yai mana jagora amin,
Karkasuwar mata

Da farko yana dakyau mufahimci cewa mata sun kasu kashi-kashi lokacin da
zasu rabu da mazajansu, saboda haka ko dole iddarsu tasha ban-ban, anan zamu fahimci mutun zai iya rabuwa da matanshi biyu ko uku lokaci guda amma wata ta riga wata kamma Idda. Yanzu ga kasha-kashannasu :
Mace me juna biyu : Alokacin da mutun ya rabu da medakinshi tana da juna biyu to ita Iddarta itace ta sauke abindake cikinta, ma'ana inda zai saketa da karfe 5:00 na yamma sai ta haihu karfe 5:20 na yammar shikenan ta kammala iddarta inta sami wanda zata aura aranar ya yi sai adaura auren da 6:00 na yammer. Yanzu ya zama dan-kallo, saidai kawai idan ya kuru Allah ya taimakeshi saki daya ne ko biyu, sai ya bogo fasta ya shiga cikin 'yan-takara wata kila ya samu ya kai labari. Allah yana cewa " Kuma wadanda suke da juna-biyu to lokacin (kammala Iddarsu shi ne ) su sauke abinda suke dauke dashi" Suratu-Talaq, aya ta :4, hakanan kuma inda zasu rabu juna biyunnata bai huce wata dayaba saidai ta haife abinda take dauke dashi, kamar yadda wannan bayanin ya gabata a ' Takaba a Musulunci' mun dan fadada bayanai a lokacin.
Mace meganin Al'ada. Itakuma matar da take ganin al'adarta iddarta itace samun tsarki uku, saboda haka idan mutun ya rabu da maidakin shi, iddarta itace ta yi tsarki uku, shi kuwa tsarki uku ya sha ban-ban da wata uku, domin mace zata iya tsarki a kwanakin da suke kasa da wats uku, haka kuma zata iya iya tsarki uku a watannin da suke sama da haka, akwai matar da ashekara sau daya take yin al'ada to kaga wannan iddarta zata tasamma shekaru kenan. Allah yana cewa " Dukkani matan da aka sakesu zasu zauna da karankansu (suna jiran) tsarki uku" Suratul-Bakara, aya ta: 228 Idan kuma tana cikin lissafa al'ada sai ya bayyana tana da juna-biyu, to anan iddarta zata koma iddar mai juna biyu saitai zaman haihuwa (Allah ya sauke ta lafiya amin).
Mace mara ganin al'ada. Matan da basa ganin al'ada sun kasu kashi biyu, kashi na farko: basagin al'adane saboda yarinta ma'ana batakai lokacin al'adaba gashi mijinta ya rabu da ita, sai kashi na biyu :wadanda basa ganin al'ada saboda tsufansu don sun wuce lokacin al'ada. To wadannan matan da basa ganin al'ada ko saboda karancin shekaru ko kuma saboda angirma, iddarsu itace su lissafa wata uku. Alllah Madaukakin sarki yana cewa " Kuma matayen da suka debe tsammani daga al'ada daga matanku idan abin ya rikice musu to iddarsu itace wata uku, da kuma ma wadanda basu fara ba" Suratut-Talaq, aya ta :4.
bMace mara ganin Al'ada: Ita matar da aka rabu da ita kafin su san junansu ita da mijin, babu wata idda da zata yi, kawai inta sami wani alokacin sai adaura aure, (sabanin rasuwa idan rasuwa mijin ya yi kafin su tare za tai takaba). Domin Allah yana cewa " Ya ku wadanda sukai Imani, idan kuka auri mata mummunai sannan kuka sake tun kafin ku sadu da su, ba ku da wata idda a kansu (matan) da za su yi" Suratul-Ahzab, aya ta :49.
Kammalawa. Ina fatan cikin wannan dan takaitaccan bayanan da suka gabata sun dan warware mana madansu al'amurran da suka shafi Idda, da kuma irin yadda musulunci ya haskaka mana rayuwarmu. Ni ina bada shawara ga dukkan wanda wadansu al'amurran addini suka shamasa kai, da kada yai kasa agwiwa ya garzaya makaranta ya yi tanbaya, masu iya maga suce 'Tambaya mabudin ilimi, amma azauna haka ko unkula gaskiya ba zai haifadda Da me ido ba, kuma wadansu hakkokinshi da damar da musulunci ya bashi ba zai sansu ba. Allah yai mana jagora kuma ya tabbar da dugadugammu kan wannan addin amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofisin 'Yansanda Minna, jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a 08020792963, ko kuma a Imei :
sadisualiyumuhammad@yahoo.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// hasken-musulunci.blogspot.com



RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI #1

RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI #1.

Gabatarwa:
Da sunan Allah Maiyawan rahama Mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halitar Allah Annabi Muhammad, da SahabbanSa da Iyalan gidanSa amin. A wannan karan zamu gudanar da bayani ne kan yadda Addinin musulunci ya tsara yadda za'a gudanar da saki, batare da ancutar da Mata ko miji ba muddindai anbi wannan tsarin. Da zaran ance saki sai gaban namiji ko mace ya fadi, ko menene dalili? Musulunci bai shara'anta sakiba don cutar da wani ban gare, asalima musulunci ya shar'anta hakanne don ceto su daga muwuyacin hali, yana daga cikin rahamar musulunci tabbatar da saki, domin yana daga cikin mizar musulunci bai yadda a cutar da kowa ba, saboda haka idan akace a zauna babu maganar cewar akwai rabuwa ga duk wanda yaga anzalince shi kuma ya yi iyakar hakurin da zai iya yi, to wannan zai ba abokin zamanshi cewar shimafa yana da gata a musulunci, da yawa akan sami na miji yana dandanawa iyalin shi azaba, to yanzu sai kace yaya?, ko kuma matar tana gasawa maigidanta aya a hannu, to ananfa dole ne asa ido domin tabbas wani na matukar cutar da dan'uwansa kuma asan wanna mataki za'a dauka, amma musulunci tuni ya dauki matakai daba-daban domin shawo kan al'amarin tun kafin yakai ga rabuwa.
Kandagarkin da musulunci ya yi.

Lalle ne musulunci ya yi kandagarki don hana rabuwar aure, ta yadda ya umarci dangin miji dana mata dasu tura wakilai guda-daga daga kowane bangare na miji da mata a lokacin da suka ga cewa lalle ka akwai sabani tsakanin wance da wane, su wadannan wakilai zasu nazarci dukkan bangarorin biyu su kuma yi kokarin daidaita al'amarin. Allah yana cewa " Idan kuka ji tsoron sabanin dake tsakanin su (miji da mata) to ku tura wani mai hukunci daga dangin sa da kuma mai hukunci daga danginta, muddin sukai nufin gyara to Allah zai daidaita tsakanisu"! Suratun-Nisa'I, aya ta :35. sanan Allah yana cewa adai cikin wannan Surar a aya ta 128 " Sulhu dai shine mafi alheri" sabo da haka a wannan bayani ya nuna mana lalle musulunci ya kula da dukkanin bangarori biyu (mata da miji), domin ganin kada rabuwa ta auku, saboda haka yana da 'yau mutun ya iya daurewa akan wani hakkinshi ya dan sassauto domin ganin ansami daidaituwa, domin daidaituwa ta fi rabuwa muddin ba akan asabawa Allah da Ma'aikinShi bane. Sauda da yawa mata sunyi hakuri da wani hakkinnasu kamar yadda mazan suma sukai hakuri da nasu domin ganin aure ya tabbata, masu iya Magana na cewa 'Tsakanin harshe da hakorima ana sabawa' wai 'zo muzauna zo musaba' saudayawa wadansu abubuwan basukai atada jijiyar wuya ba sai kaga za'a ba hammata iska, Allah ya sawwake.

Adadin Saki
!

Idan Allah ya kaddari sai an rabu tofa ba makawa sai hakan ya faru, to amma ya addinin musulunci ya tsara yadda sakin zai kasance? Kafin zuwan addinin musulunci mutanan jahiliyya sun kasance suna sakin mata yadda suka dama
ba wani adadi, sannan idan mijin ya ga ta kusa kamma idda sai ya dawo da ita, wannan ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, yazamana suna azabtar da mata akan wannan mummunar al'ada, sai mace ta zauna shekara-da- shekaru ita ba mai mijiba kuma ba kuma mara mijiba, domin idan ya saketa ta kusa kamala idda sai ya dawo da ita, idan aka dan kwana biyu sai ya sake sakinta, da musulunci ya zo sai yai wa tufkar hanci, domin gallazawa mata a irin wannan bai kamata ba, musulunci yace ' Sakin da zai yiwu ai komai akanshi karo biyu ne' Suratul-Bakara, aya ta :229. anan sai aka nuna mana mutun zai iya sakin medakinshi kuma ya iya yin kome karo biyu, anan wata hikima ta musulunci sai yace saki sau biyu, domin ya nuna maka cewa abin da akafi so shine kayi daya sannan kasake yin dayan domin idan kai biyun lokaci guda tofa damarka ta kome daya ce ba biyuba, sabo da haka har idan ya zama ba makawa to sai kai dayan domin wata damarkace ka ajema kanka. Idan kai kake da laifi zaka gane idan kuma ita ce zata fadaka, idan ba hakaba sai ka kara gudan wani lokaci ya zama biyu kenan, to daga nan sai kowa ya shiga taitayinshi ya kuma kula da hakkokin da musulunci ya dora akan kowannensu domin ana kara saki na uku to ba kome ba biko sai kuma wani jikon, domin sai ta kammala idda ba kuma a gidanshi ba, sannan sai ta auri wani mijin ya dan-daneta ta dan-daneshi tasu ta hadasu sun rabu ko ya rasu sannan ya fito cikin 'yan-takara, dirkashi! Domin Allah maigirma da daukaka yana cewa " To idanfa ya saketa (saki na uku) bata halatta a gareshi hassaita auri wani mijin da ban" Suratul-Bakara, aya ta : 230. Kuma bayani ya tabbata daga Ma'akin Allah cewa saisun dan-dani juna. idan kai laka'ari ai anbashi damar yabi a hankali amma yai gaggawa, zaka ga wani duka biyun yake yi lokaci guda wani ukumma kwata-kwata kenan (malam mai gaba daya) sannan ya zo yana neman wai malamai su yi mishi fatawar yiwuwar dawo da ita, dankari!. Yanzudai saki ya auku to menene abinyi?
Idda

Idan sakin da akai bai wuce daya ko biyuba to matar zatai iddar ta ne a dakinta, bai halatta miji ya fitar da ita daga dakin, balle har ya watso mata kayan ta waje ko ya dakko mota akwashe mata kayanta, ko kuma ita tace ai tana da gidan ubanta bari ta tafi da dai sauran irin wadannan kazaman maganganu da musulunci bai amince da su ba, Allah Yana cewa " Kada ku fitar da su daga dakunan su, su kuma kada su fita sai dai idan sunzo da wata alfasha bayyananniya, dukkan wadannan dokokin Allah ne kada ku ketare su, dukkan wanda ya ketare dokokin Allah tofa hakika ya zalinci kanshi" Suratut-Talaq, aya ta :1, to anan zakaga lalle irin yadda ake gudanar da rabuwar aure hakika abin yana bukatar gyara sosai wannan fa gamu musulmai da muka yadda da dokokin da Allah ya dora mana, ya Allah ka yafe mana, kuma ya Allah kada ka kamamu da abinda wawayencikimmu suka aikata, amin. Me cece hikimar yin hakan mace tai idda a cikin dakinta?
Hikimar Idda a dakin aure.

Lalle ne dukkan abinda Allah madaukakin Sarki ya tsara mana akwai hikimomi da alherai masu yawa agaremu munsani ko bamu sani ba, kuma ba'a dora mana cewa dole sai munsan hikimar hakan kafin mu ai watar da abida aka umarce mu. Tabbas mutuminda ya rabu da medakinshi ta hanyar saki yada ko biyu, matar shi ce fa , domin inka lura ai ba zaka bar wani ya zo zawarciba, inkuma ka rasu a wannan lokacin kafin ta kamma idda zata gajeka, kuma zatai maka takaba (kamar yadda ya gaba a makalarmu metaken Takaba a musulunci) to anan tunda tana Idda a gidanka zaka dawo da ita aduk lokacin da kaso ba tare da ansake daura aureba domin bata kamala Iddaba, kuma ba saika ta tuttura masu bikoba, wannan shi ne ma'anar fadin Allah daya ke cewa "Baka sani ba ana fatan Allah ya kawo wani sabon al'amari" Suratut-Talaq, aya ta :1, to amma sai wannan damar da Maigirma da daukaka ya bamu itama ana wasa da ita, bayan da mutun ya sabawa Mahaliccin shi sannan matar tana nema ta gagareshi, galibi kuma alokacin ba wacce yake so inba itaba, dabara kaga tana neman ta karewa kada. Saidai kamar yadda ishara ta gabata a baya matar da zatai idda a dakinta itace matar da saki daya ko biyu ya rabasu amma matar da saki ukune nan ba magar yin idda a dakinta, saigida!. Saidai akwai abin tanbaya anan shin akowanne lokaci ya halatta mutun ya rabu da medakin shi?.
Lokotan Saki da musulunci ya amince da su
.

Anan nake ceawa lalle yana daga cikin irin gatan da musulunci ya nuna mana cewa ba'a sakin mace lokacin da take cikin al'ada. Kuma idan mutun ya aiwatar da sakin ta saku kuma dole ya mayar da ita cikin matanshi, inyaki kuma alkali ya hukunta shi, sabo da Sayyidina Umar Allah ya kara masa yarda ya tambayi Ma'aikin Allah Tsirada amincin Allah su tabbata agareshi, cewa danshi Abdullahi ya saki matar tana ckin al'ada. Sai Ma'aikin Allah ya umarci Sayyidina Umar daya umarci dannashi Abdullahi ya dawo da ita, sannan tana karkashinshi hassai ta kammala wannan al'adar ta sakeyin wata ta kammala sannan in yaga yiwuwar ya saketa sai ya saketadin, kuma aka lissafa wannan sakin cikin sakinna shi, Bukhari ya ruwaito wannan hadisin kuma shine hadisi na : 4908, 5252 ,5253 da Muslim. To idan mutun ya saki matarshi shikenen ba dai za'a raba kirki da itaba, ma'ana bata cikin matan da za'ai karba-karban girki da su, to haka za'a kyaleta? A'a za'a bata :
Kwabo kashewa.

Yana daga cikin hakkin dukkar matar da mijinta ya saketa da ya bata kwabon batarwa, wannan shine malamai suke kira Mut'atuttalaq, domin zata sai sabulu omo katin waya da dai sauransu, musulunci bai kayyade gwargwadon nawa za'a bayarba saidai ya fadi a wurare da dama kowa zaiyine daidai karfinshi, sabo da haka mutumin da yake da damar yaba wacce ya saka Naira dubu 40, misali sai yabata N 10,000, wannan bai yiba sai ya cika ko ta kaishi koto, haka kuma mutumin da bashi da karfin haka baya taba halatta a tilasta mishi sai ya bayar da hakan, musulunci cewa yayi kowa daidai karfin shi, Allah yana cewa cikin Suratul-Bakara aya ta :236 "Kuma ku jiyar da su dadi, me yalwa gwargwadon karfinshi, kuma mara yalwar arzikima gwargwadonshi" ayoyi akan baiwa matar da aka saka kudin kashewa sun memetu a wannan surar aya ta :241 da Suratul-Ahzab,aya ta :28 data 49, duk wadannan suna daga cikin dinbin ayoyin Alkur'ani mai girma da suke ceto mata daga cikin bakin kangin da suka sami kansu a tsarin da bana musulunci ba. kasancewar al'amarin rabuwar aure ba haka yake sakakaba. Kamar yadda alokacin daurin auren saida aka sami shaidu to hakama lokacin rabuwar saida musulunci yabada umarnin.
Shaidawa Dattijai biyu

Abin sanine cewar Dattijai yana nuna mutanan kwarai mutane masu mutunci masu yawan shekaru ko masu matsakaicin shekarune muddin sunkai shekarun girma da sanin ya kamata, saboda haka musulunci yabada umarni shaidawa akalla Dittijai biyu domin tabbatar da saki nawa akai kuma nawa ya rage, amma inba hakaba sai aita gardaddami akan nawa ya auku kuma nawa ya ragedin, Allah Maigirama da daukaka yana cewa " Kuma ku shaidawa Adilai biyu daga cikinku, ku tsayar da shaidar domin Allah" Suratut-Talaq, aya ta:2. to kan lalle akwai kulawar musulunci cikin dukkanin motsi da juyi da Dan-adam yake yi, ya Allah ka tabbatar damu akan wannan addini naka amin.
Kome \ Biko.

Kome kamar yadda bayanai suka gabata yana kasancewa ne lokacin da mutum ya rabu da medakinshi ta sanadiyyar saki daya ko biyu, anan mutun ke kokawar yaga ya mayar da matarshi, amma idan ya kasance sakin saki ukune to kan ai ba maganar biko balle kome. Shi wannan al'amari na kome yana faruwane kafin matar ta kammala Idda, amma idan ta kammala Idda tofa saidai da sabon aure tunda sakin baikai ukuba, amma indai ya kai uku to sai ta yi sabon aure, saboda haka tunda saki dayane ko biyu kuma ta kammala idda bai dawo da itaba to yanzu sai ya fito cikin 'yan-takara, idan Allah ya sa ya kai labari to idan kuma ya sha kaye sai hakuri. Amma idan bata kammala Iddaba to mijin shi ke da damar ya mayar da ita ba tare da wani ya yi kaka gida cikin lamarinba muddindai sunyi nufin gyara(wato miji da mata) Allah Maigirma da daukaka yana cewa "Kuma mazajansu sune mafi cancantar su mayar da su (matansu) matukar sunyi nufin gyara" Suratul-Bakara, aya ta : 228, wannan shike nuna cewa duk lokacin da miji ya mayar da matar muddin akwai nufin gyara babu wani ta koma kawai.
Kammalawa
Daga dukkanin bayanan da suka gabata bayanai sun bayyana karara na gata da jinkai da musulunci ya yi mana, domin babu wani tsari a duniya da yake da irin wannan al'amari filla-filla ya fayyace tsakanin zare-da-abawa, musammamama mata, domin zakaga duk wani tsari da ba musulunci ba to bautar dasu yake kai tsaye ko a fakaice, amma lalle musulunci ya yi mata gata saidai idan ta jahilceshi wannako babbar cuta ce, Allah ya tsaremu amin.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofisin 'Yansanda Minna, jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a 08020792963, ko kuma a Imei :
sadisualiyumuhammad@yahoo.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// hasken-musulunci.blogspot.com

الجمعة، 11 يوليو 2008

TAKABA A MUSULUNCI

HASKEN-MUSULUNCI.blogspot.com
Don bayyana yadda Musulunci ya haskaka mana dukkanin rayuwarmu

TAKABA A MUSULUNCI
Gabatarwa:

Da sunan Allah Maiyawan rahama Mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halitar Allah Annabi Muhammad, da SahabbanSa da Iyalan gidanSa amin. Muna son a wannan lokacin muyi bayanin yadda addinin musulunci ya haskaka duhun da duniya ta dade aciki, ayayin yin takaba lokacin da mace megidanta ya rasu, ta yadda kowacce kabila take yi yadda ta tashi taga haka mutananta ke yi , a irin wanna lokacinne mata suke dan-dana kudarsu, domin suna kan wani tsari da Allah Madaukakin sarki bai turo wani Annabi da wannan tsarinba. Ayau zamuyi kokarin fayyacewa tsanin zare da abawa ne, akan yadda takaba take a musulunci, da kuma irin gatan da musulunci ya yi wa mata. Asha karatu lafiya Allah yai mana jagora amin.
Mecece Takaba?: Tabadai itace" Zaman da mace zatayi bayan rasuwar megidanta na wadansu kwanuka sanannu, batare da ado da kwalliya ba, ba kuma da yin wani aure ba, ko sanya dukkan abinda zai ja hankalin wani ba, na tufafi ko kayan karau." Awanna bayani daya gabata zamu tsinkayi abubuwa masu yawa, wadanda kusan za mu bisu a hankali gaba-gaba domin fayyace su.(anan Takaba ta sha babban da Iddar saki, wadda muke fatan a wani lokaci muyi bayaninta, in Allah ya yarda)
Wacece mai yin Takaba?: Matar da zatai zaman takaba, itace dukkar matar da mijinta ya rigamu gidan gaskiya, tana matarshi, sunyi saduwar aure ko busu yi ba!. Anan zamu fahimci cewa muddin akwai igiyar aure a tsakanin su, to za tai takaba. Misali (Allah ya kiyaye) inda aka daura auren mutun da karfe 2:30 na rana, sannan bayan minti 30 ko awa guda ya rasu, to fa takaba ta ganta, kuma zata ci gadonshi, domin matar shice. Kamar yaddau Abdullahi Dan Mas'ud Allah ya kara masa yarda, ya bada amsa lokacin da aka tanbaye shi akace da shi : Mutunne ya auri mace amma bai bayyana mata sadakinta ba, kuma bai sadu da ita ba har ya rasu? Sai Dan Mas'udin ya ce" Zan bada amsa da fahimta ta, idan na yi daidai to daga Allah ne, idan kuwa banyi daidai ba to daga Shaidan ne, Allah da Ma'aikin Shi sun barranta da wannan amsar. Tana da sadakin mata ire-irenta, ba kari ba ragi, kuma za tai Takaba, sannan tana da gado". Sai Ma'akil Dan Sinan wanda yake daga kabilar Ashja'a ya mike yace: "Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, ya yi irin wannan hukuncin da kayi ga Rauh Diyar Washik –wata mace ce daga cikin mu, sai Abdullahi Dan Mas'ud yai farinciki da wannan Magana tashi" Imam Ahmad da Abu-Daud da Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah suka ruwaito wannan hadisin, kuma Tirmizi ya Inganta shi. Hakanan kuma inda mutun zai rabu da mai dakinshi da saki daya ko biyu, sannan ya rasu kafin ta kamma iddar saki, shikenan sai ta koma takaba, matarshi ce yana da dama yado da ita a ko yaushe muddin bata kammala idda ba.
Gwargwadon kwanakin Takaba: Alokacin da mutun ya rasu, to zaibar iyalin shi a dayan halaye biyu, kodai ta zama tanada Juna biyu ko kuma bata da shi. Idan bata da juna biyu to Takabarta itace "Wata hudu da kwana goma" Kamar yadda Allah yace cikin Suratul-Bakara "Kumma dukkanin mazan dake rasuwa daga cikin ku subar matayansu, to matan zasu zauna wata hudu da kwna goma" aya ta :234 To amma idan ya rasu ya barta da juna biyu, a wannan lokacin karshen Takabarta shine ta sauke abinda take daoke da shi, koda ko ranar da ya rasu ne, Misali ya rasu 7:00 na safe ita kuma ta haihu 7:10 na safiyar, shi kenan ta kammala takabarta, idan wani ya gani yace yana so aka daura aure 2:30 na ranar aure ya dauru(ana karbar gaisuwa ana daurin aure) dalii kuwa shi ne. fadin Allah a cikin Suratut-Talak aya ta 4 " Kuma dukkanin mata masu juna biyu to lokacinsu shine su sauke abinda suke dauke dashi" da kuma Hadisin Subai'a Al-aslamiyyah, " Ita ta kasance tana auran Sa'ad Dan Khaulah, shi kuma ya fito ne daga gidan Amir dan Lu'ayy, yana daga cikin wadanda suka halarci gwabzawar Badar, sai ya rasu yabarta a hajin bankwana tana da juna biyu, bata ko jima ba bayan rasuwar shi saita haihu, a lokacin data kamma biki sai tai kwalliya, sai Abu-Sanabil Dan Ba'akk yazo wurinta, shi kuma ya fitone daga gidan Abduddar, sai yace da ita " Lafiya naga kin cancara ado, ko kina son ki aure ne? Na rantse da Allah lokacin auranki bai yi ba, harsai kin yi wata hudu da kwna goma. Sai Subai'a tace "Yayinda ya fadi min haka maraice na yi sai na tattara kayana naje wurin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, na tambaye shi hakan, sai ya ban amsa da cewa ai na kamala Takabata tun lokacin dana haihu, ya ban dama da inyi aure a duk lokacin da naga dama". Wanna hadisin Bukhari ya ruwaito shi, hadisi na 4909 da kuma na 5318, hakanamma Muslim da Abu-Daud da Tirmizi da Nasa'I, da Ibnu Majah. Inbu Shihab yake cewa : "Bana ganin akwai wani laifi idan ta yi aure lokacin data haihu, koda tana cikin jinin biki, saidai kawai mijin ba zai kusanceta ba sai ta yi tsarki. To haka kuma idan yarasu ya barta da juna biyu na kimanin wata daya ko ma baikai haka ba, tofa sai ta haihu kaga wannan Takabarta na neman wata tara koma fiye kenan domindai saita sauka. Zai iya yuwuwa alokacin da maigida yarasu bata samma tanada juna biyu ba, wata kila a saduwarda bai huce masa saura minti 30 aduniya ba ta sami juna biyun, to kaga wannan zata fara lissafin kwanaki ne na Takaba sai daga baya Takabarta ta koma sauraran haihuwa, Allah ya sauketa lafiya shi kuma maigida Allah yajikan shi. Wannan ya nuna mana cewa mutun zai iya rasuwa ya bar matanshi, amma wata ta riga wata kamala Takaba, domin musulunci bai yadda a dauki dan wani gida akai wani gida ba, wannanfa ko da mace mai Takaba ta samu kwanciyar ciki, domin ciki yakan kai shekara 4 ko 6 kamar yadda malai sukai bayani, duba Tafsirin Adhwa'ul Bayan Suratur-Ra'ad aya ta :8. Abinda ake nufi data sauka shi ne, ta sauke duk abinda ke cikinta, ya zo da rai ko bai zo da rai ba, saboda haka ko bari tayi ta kamala idda idan aka samu shaidu akan hakan, koma ace siffar mutun ta bayyana a tare da shi barin, idan mai Takaba ta haihu sannan ingantaccen bincike yanuna cewa tana dauke da 'ya'ya biyu ne kuma gashi ta haifi daya, tofa bata kammala ba sai ta haifi na biyun, domin abinda ake bukata ta sauke duk abinda take dauke da shi.
Yaushe za'a fara lissafin Takaba?. Za'a fara lissafin maitakabane daga lokacin da megida ya rasu, ba wai kamar yadda akebin al'ada ba wai sai ran juma'a, ko dako ya rasu ranar asabar, sannan ai mata wankan shiga Takaba, wannan kwata-kwata ba shi da alaka da addinin musulunci, sannan ace za'aba maitakaba wuka ko sanda, in zata shiga makewayi ta rike, kuma ta tafi a hankali wai mijinta na biye da ita, a firgita baiwar Allah. Saboda haka daga ranar da mijinta ya rasu daga ranar ta fara idda, yana rasuwa ta shiga Takaba. Saboda haka idan ya rasu bata sami labarin rasuwarshi ba, sai bayan wata hudu da kwana goma, ko bayan haihuwarta sannan ta sami labarin shikenan ta kamala takabarta, in kuma bayan wata biyune da rasuwar shi ta sami labarin rasuwarshi to yanzu Takaba ta rage mata wata biyu da kwana goma. Sannan kuma babu wani wankan fita daga Takaba a mulunci, da zaran ta kammala wata hudu da kwana goma, ko ta haihu to ta kammala Takaba, saboda haka duk abinda ya haramta agareta lokacin tana Takaba to yanzu ya halatta ta yi domin ta kammala takaba.
To me ya haramta ga maitakaba? A dunkule abinda ya haramta ga maitakaba shine 'Ado da kwalliya, da kuma in aure ko yiwa wani al'kawari, ko fita ba tare da wani dalili na Shara'a ba. anan yana da kyau mu banbance tsakanin Kwalliya da Tsafta ya haramta tai kwalliya da ado, kamar sa Tozali, Kunshi, sa hoda yin dizayin janfarce janlebe, sanya tufafi na ado sa ture –indai ba bayan ta kammala al'ada ta diga shi akyalle domin tasa agabanta saboda rage karnin jiniba- da dai dukkan wani nau'I na ado ko kwalliya, koda ko rangada kitsone. Amma ita tsafta babu wanda ya hana maitakaba yinta, yin wanka kullun yin kitso idan bukatar hakan ta taso ba kuma ayi don kwalliyaba, suma sun san na kwalliya kuma kun san wanda za'adan kakkama alallaba, kuma ya halatta tayi wanki domin duk suna cikin tsafta ba kulliyaba, sannan ya halatta ta share dakinta ba ta zauna kamar wata mai haukaba, sannan dukkanin wadannan abubuwa babu wata rana da aka ajeye musu don gudanar da su, kamar ace 'sai juma'a ko laraba' za ta yi aduk lokacin da bukatar hakan ta samu. Anan nake cewa lallai akwai babbanci wanda ba zai yiwu ahadaba da irin yadda musulunci ya fayyace mana al'amura dalla-dalla ya haskaka mana su, da kuma irin yadda al'adu sukai kane-kane cikin harkar Takaba, Allah ya sauwake.
Kammalawa: daga dukkanin bayanan da suka sauwaka zamu fahimci irin gatan da musulunci ya yi mana shi irin saukin da ya nema mana, musamman idan muka kalli yadda Allah ya tsara mana kuma muka kalli yadda ake a al'ada lallai zamu fahimci ya zama wajibi mudada godewa Allah akan wannan ni'ima da yayi mana.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofisin 'Yansanda Minna, jahar Neja.
Za'a iya tuntuba a 08020792963, ko kuma a Imei : sadisualiyumuhammad@yahoo.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// hasken-musulunci.blogspot.com

Littafan da aka duba.
1- Alkur'ani Maigirma.
2- Tafsirin Ibnu Kasir
3-Adhwa'ul-Bayan Na Muhammad Amin As-Shankiti
4- Ahkamul-Kur'an Na Ibnul-Arabi
5- Fat'hul-Bari Na Ibnu-Hajar
6- Al-Mughni Na Ibnu Kudama
7- Taisirul-Allam Na Abdullahi Bassam.